Featured
Za mu cigaba da gabatar da ayyukan alherin da muka ga magabatanmu suna yi – Aminu Bayero
Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero yace za su cigaba da dorawa akan dukkan abubuwan da magabatansu suka bari domin wanzar da alkhairai ga al’uma.
Aminu Bayero ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin zauren Limaman Masallatan Hamsa salawati da Na’ibansu da Makarantun Tsangayu da Islamiyyu a fadarsa dake Gidan Nassarawa a Birnin Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace yanzu ana cikin wani zamani da lalacewar abubuwa suke neman tabarbarewa musamman tarbiyya da da’ar al’umma bisa la’akari da yadda ake samun tabarbarewar hakan a cikin al’uma.
Ya bukaci kungiyar su cigaba da kula da tarbiya da da’ar al’umma da cigaba da yin addu’oi domin Allah ya daidaita wadannan al’amura tare da cigaban dorewar zaman lafiya da wadatar arziki a jihar Kano da Kasa baki daya.
Da yake gabatar da jawabi Shugaban Zauren Malam Muhd Bashir Aliyu yace sun je fadar ne domin nuna Mubaya’arsu tare da godiya a gareshi bisa irin ayyukan alherin da yake gabatar musu wadanda suka hadar da gyaran masallatai da makarantun Islamiyya da kula da marasa lafiya.
Malam Muhd Bashir ya tabbatarwa da sarkin cewa za su cigaba da yin biyayya da nuna goyon bayansu a gareshi da kuma cigaba da gabatar da addu’oi domin samun nasorori da cigaba da kuma wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Sa hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren Yada Labarai na Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, CFR, JP, CNOL
28/05/2025
