Connect with us

Featured

Fiye Da Mutum 10, 000 Aka Kashe A Shekaru Biyu Na Mulkin Tinubu – Amnesty International

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan nan ya nuna cewa, cikin shekaru biyu da kafuwar gwamnatin Tinubu, an kashe aƙalla mutum 10, 217 a hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihohi daban-daban.

Jihohin sun haɗa da Benue da Edo da Katsina da Kebbi da Plateau da Sokoto da Zamfara.

Jihar Benue ce ke da mafi yawan adadin mutanen da aka kashe – inda ya kai har mutum 6,896, sai Jihar Plateau da mutum 2,630.

Amnesty International, ta fitar da wannan rahoto ne a dai dai lokacin da Shugaba Tinubu ke cika shekaru biyu a kan ƙaragar mulki, inda ta zargi gwamnatinsa da gazawa wajen kare rayukan ‘yan kasa da kuma gurfanar da waɗanda ke da hannu a aikata laifuka duk da alkawurran da gwamnatin ta sha yi na inganta tsaro.

Rahoton ya kuma bayyana cewa “an raba ɗaruruwan ƙauyuka da muhallansu musamman a Zamfara da Benue da Plateau, inda dubban mutane suka rasa matsugunansu.”

“Hare-haren sun kuma lalata ababen more rayuwa da suka haɗa da rijiyoyin burtsatse da makarantu da asibitoci wanda hakan ya kara tsananta halin da jama’a ke ciki.” A cewar rahoton.

Amnesty International ta kuma yi gargadin cewa korar manoma daga gidajensu na kara haddasa yunwa da talauci.

A jihar Plateau, an bayyana cewa mutum 65,000 ne suka rasa matsugunansu, a Benue kuwa adadin ya kai 450,000.

“Sababbin ƙungiyoyin ‘yan bindiga da suka hada da Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi, da Mamuda a Kwara, na kara tsananta rikici.” in ji rahoton

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa domin dakile irin waɗannan hare-hare da kisan gilla, tana mai cewa “lokaci na kurewa, yayin da hare-haren ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya ke kara tsananta.”

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet