Featured
Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Hutu Domin Jimamin Ƴan Wasan Da Suka Rasu
Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya ayyana ranar Litinin 02 ga watan Mayun 2025 a matsayin ranar jimami a jihar, inda ya amince da ba ma’aikatan jihar hutun aiki domin alhinin waɗanda suka rasa ransu daga cikin tawagar ƴanwasanta da suke yi hatsari a hanyarsu ta komawa gida daga wasannin ƙasa da aka yi a Ogun.
Zuwa yanzu kimanin mutane 22 ne suka rasu daga cikin tawagar, yayin da wasu kuma suka jikkata.
A sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya kaɗu matuƙa da samun labarin mutuwar ƴanwasan.
“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, muna miƙa ta’aziyarmu ga iyaye da iyali da ƴanuwan waɗanda suka rasu. Sanan ina kira ga dukkan musulmi a jihar da su yi addu’ar samun rahamar Allah ga waɗanda suka rasu.” A cewar sanarwar.
Gwamnan ya kuma ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen kula da waɗanda suka jikkata, da kuma tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu.
