Connect with us

Featured

NIMET Ta Yi Hasashen Ruwan Sama Da Iska Mai Ƙarfi Daga Litinin Zuwa Laraba

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen ruwan sama tare da iska mai ƙarfi tsawon kwanaki uku, tun daga yau Litinin 02 ga Yunin 2025, zuwa Laraba 04 ga Yunin 2025 a fadin kasar.

A cewar rahoton yanayi da hukumar ta fitar ranar Lahadi a Abuja, an yi hasashen za a samu iska mai ƙarfi tare da ruwan sama a safiyar Litinin a wasu sassan jihohin Taraba, Kaduna, Gombe, Bauchi, Kebbi, Sokoto, Katsina, Jigawa da Kano a yankin Arewacin Najeriya.

A yankin Arewa ta Tsakiya, an yi hasashen za a samu iska mai ƙarfi da ruwan sama a wasu sassan Babban Birnin Tarayya (FCT), Neja da Nasarawa duk a safiyar Litinin.

Duka dai a yammacin Litinin din, ana sa ran iska mai ƙarfi da ruwan sama a wasu sassan Filato, FCT, Nasarawa, Kwara, Neja, Kogi da Benue.

“A yankin Kudancin Najeriyakuwa, an yi hasashen za a samu yanayi na hadari da ruwan sama a wasu sassan Ondo, Ogun, Edo, Ebonyi, Abia, Cross River, Rivers da Akwa Ibom a safiyar Litinin,” a cewar rahoton.

Da rana kuma, hukumar ta ce ana sa ran ruwan sama a wasu sassan Oyo, Ekiti, Ogun, Osun, Ondo, Legas, Edo, Abia, Imo, Ebonyi, Enugu, Anambra, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, Delta da Bayelsa

Ranar Talata kuwa, a ArewacinNajeriya, an yi hasashen za a samu iska mai ƙarfi tare da ruwan sama a wasu sassan Kano, Zamfara, Katsina, Bauchi, Gombe, Adamawa, Borno, Yobe da Taraba a safiyar ranar.

“Da yammacin rana, ana sa ran iska mai ƙarfi da ruwan sama a wasu sassan Taraba, Kebbi, Borno, Gombe, Adamawa, Kaduna, Bauchi da Katsina,” a cewar rahoton.

A yankin Arewa ta Tsakiya, hukumar ta ce za a samu iska mai ƙarfi da ruwan sama a safiyar ranar a wasu sassan FCT, Neja da Nasarawa.

Yayin da bayan rana ta yi, ana hasashen iska mai ƙarfi da ruwan sama a wasu sassan FCT, Nasarawa, Kogi, Neja, Kwara da Filato.

A Kudu, an yi hasashen za a samu iska mai ƙarfi tare da ruwan sama a wasu sassan Ondo, Ogun, Edo, Ebonyi, Abia, Cross River, Rivers da Akwa Ibom a safiyar ranar.

Hakanan da rana kuwa, an yi hasashen ruwan sama a wasu sassan Oyo, Ekiti, Osun, Ogun, Legas, Edo, Anambra, Abia, Enugu, Imo, Ebonyi, Cross River, Rivers, Delta da Bayelsa.

A ranar Laraba kuma, hukumar ta yi hasashen za a samu iska mai ƙarfi tare da ruwan sama a safiyar ranar a wasu sassan Zamfara, Adamawa, Kaduna, Sokoto, Kebbi da Taraba.

Yayin da da rana, an yi hasashen iska mai ƙarfi tare da ruwan sama a wasu sassan Taraba, Kaduna, Katsina, Bauchi, Zamfara, Sokoto da kuma Adamawa.

“A Arewa ta Tsakiya, ana hasashen iska mai ƙarfi tare da ruwan sama a wasu sassan FCT, Nasarawa, Neja da Benue a safiyar ranar.

“Bayan rana ta fito kuma za a samu iska mai ƙarfi da ruwan sama a wasu sassan Nasarawa, Filato, FCT, Kwara, Kogi da kuma Neja.

“A Kudu, ana hasashen ruwan sama a wasu sassan Ogun, Ondo, Oyo, Edo, Enugu, Ebonyi, Cross River, Rivers da Akwa Ibom a safiyar ranar.

“Hakanan, ana sa ran ruwan sama a dukkan sassan yankin da rana,” a cewar rahoton.

NiMet ta gargadi jama’a cewa akwai yiwuwar samun iska mai ƙarfi kafin zuwan ruwan sama a wasu yankuna, don haka ya kamata kowa ya dauki matakan kariya.

Hukumar ta kùma shawarci jama’a su tabbatar da cewa sun kulle dukkan abubuwan da iska ka iya dauka, su guji tukin mota yayin ruwan sama mai yawa, su cire na’urorin lantarki daga soket, da kuma nisanta kansu daga manyan itatuwa don guje wa hadarin reshe ko itatuwan da ka iya karyewa.

“Masu aikin jirgin sama su tabbatar sun samu bayanan yanayi na filin jirgi daga NiMet domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet