Featured
Adadin Wadanda Suka Mutu A Ambaliyar Mokwa Sun Haura 200 Yayin da Mutum 500 Su Ka Yi Ɓatan-Dabo
Zuwa yanzu adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar da ta afku a garin Mokwa, karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja a ranar Laraba da ta gabata, ya kai 200 yayin da wasu fiye da 500 suka bace.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ambaliya ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, inda ta shafi unguwannin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa bayan ruwan sama mai yawa da ya sauka da daddare.
Tuni dai ɗaruruwan gidaje suka lalace, yayin mutane da dama suka rasa matsugunansu.
BBC ta rawaito cewa adadin wadanda suka mutu ya zarce 200, yayin da fiye da 500 har yanzu ba a gan su ba.
A cikin wadanda ambaliyar ta shafa akwai mata da yara, ciki har da daliban makarantu na Qur’ani.
Musa Kimboku, wani jami’i a yankin, ya shaida wa BBC cewa a halin yanzu an dakatar da aikin ceto, saboda hukumomi sun yi imanin babu sauran wanda za a iya samu da rai.
Hakazalika, dagacin Mokwa, Muhammadu Aliyu, ya bayyana cewa za su fara tono gawawwaki da aka binne don kauce wa yaduwar cututtuka a yankin.
Ya ce wasu gawawwakin ba za a iya gano su ba saboda ruwan ya yi awon gaba da su zuwa Kogin Neja.
