Featured
Rundunar Ƴan Sanda Ta Sanar Da Ƙarin Wa’adin Fara Tilasta Yin Lasisin Gilashin Mota Mai Duhu Zuwa Watan Agusta
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta sanar da ƙarin wa’adin fara tilasta samun lasisin gilashin mota mai duhu ( Tinted Glass) zuwa ranar 12 ga watan Agusta, 2025, bayan samun korafe-korafe da ra’ayoyi daga jama’a.
Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Asabar 14 ga Yuni, 2025. Inda ya ce an ɗauki matakin ne domin sauƙaƙa tsarin neman lasisin ga ‘yan ƙasa.
A cewar sanarwar, wannan mataki na nuna yadda rundunar ke da niyyar yin aiki da gaskiya, ta hanyar haɗa kai da al’umma tare da bai wa kowa dama a cikin tsarin aikin ta.
Rundunar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba da dama a ƙara inganta tsarin aikace-aikacen – ta fuskar na’ura da kuma na zahiri – ciki har da tantance bayanai cikin sauƙi da rage jinkiri.
An shawarci ‘yan Najeriya da su nemi ko sabunta lasisinsu ta hanyar shafin yanar gizon hukuma kawai, kuma su kai rahoton duk wani abu da ya shafi cin hanci ko karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba yayin aiwatar da tsarin.
Rundunar ‘Yan Sanda ta kuma sake jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyi, da kuma inganta aikinta ga jama’a. Ta kuma bukaci al’umma da su ci gaba da bayar da goyon baya yayin da ake ci gaba da gyare-gyaren tsarin.
