Featured
2027 : Tinubu Ne Ke Da Alhakin Zaɓar Wanda Zai Yi Masa Mataimaki – Mataimakin Shugaban APC na Arewa Maso Gabas
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Yankin Arewa Maso Gabas, Mustapha Salihu, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan makomar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a zaben 2027 mai zuwa.
Salihu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Litinin 16 ga Yuni, 2025.
A ranar Lahadi ne wata hatsaniya ta tashi, bayan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC daga yankin Arewa Maso Gabas sun amince da sake tsayawa takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 ba tare da ambato Mataimakin sa Shettima ba.
Sai dai a hirar da aka yi da shi, Salihu ya ce jiga-jigan APC na Arewa Maso Gabas sun goyi bayan Tinubu ne ba tare da sharadi ba.
A cewar sa “Ba za mu ce saboda dan mu ne Mataimakin Shugaban Ƙasa, mu ce sai mun goyi bayan Asiwaju da sharadi ba. Ba za mu yi hakan ba. Muna mara masa baya ba tare da wani sharadi ba. Doka ta bayyana cewa tikiti ɗaya ne ake da shi, ba mu da tikitin Mataimakin Shugaba. Idan muka ce mun goyi bayan Kashim Shettima, kamar mun saka wa Asiwaju magana a baki, kuma hakan abu ne da bai kamata a gabatar ba.”
“Muna alfahari da Kashim Shettima a matsayin ɗan mu, muna girmama shi kuma muna tsaye tare da shi. Amma Asiwaju ne kaɗai ke da ikon yanke hukunci ko Shettima zai kasance abokin takararsa ko a’a. Amma ba za mu mara wa Asiwaju baya tare da wani sharadi ba.”
