Featured
Ƴan Sanda A Kano Sun Kama Mutane 51, Tare Da Ƙwato Makamai Da Miyagun Kwayoyi
Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa ta kama mutane 51 tare da kwato makamai da miyagun kwayoyi a wani samamen kamen ‘yan daba da masu aikata laifuka wanda aka gudanar a cikin birnin Kano.
DSP Hussaini Abdullahi, Mataimakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin 16 ga Yuni 2025, inda ya ce samamen ya ɗauki tsawon kwanaki uku – daga Juma’a zuwa Lahadi – a yankunan karamar hukumar Birnin Kano, Dala, Gwale da Tarauni.
Ya ce yankunan da aka kai samamen sun haɗa da Kofar Mata, Zage, Kurna, Rijiyar Lemo, Dorayi, Hotoro da Sheka.
“Wannan aiki na daga cikin kokarin da rundunar ke yi wajen kawar da matsalar ɗaba da laifukan da suke da alaƙa da ita a fadin jihar,” in ji DSP Hussaini.
Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya ja kunnen matasa da su guji amfani da makamai a lokutan shagulgulan gargajiya kamar “Kidan Gangi.”
Kwamishinan ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ta nuna makamai a dandalin sada zumunta kamar TikTok, Facebook, X (Twitter), da Instagram.
“Nuna makamai a dandalin sada zumunta yana ƙara ta’azzara laifi, tare da janyo hankalin matasa su fada cikin mugayen kungiyoyin. Duk wanda aka kama yana wannan aiki zai fuskanci hukunci,” in ji Bakori.
Haka zalika, ya gargadi iyaye, masu renon yara da masu sana’ar ƙirƙira makamai da su daina taimakawa wajen mallakar makamai, yana mai cewa shima doka za ta hukunta su idan aka kama su da laifi.
Bakori ya bukaci jama’a da su kasance masu lura da abin da ke faruwa a muhallinsu tare da sanar da hukumomi duk wani abu da suke zargi, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.
