Connect with us

Featured

Kano Online Chapel Ta Fara Sayar Da Fom Ga Masu Sha’awar Shiga

A kokarinta na hada kan ’yan jarida masu aiki a kafafen yada labarai na zamani da yanar gizo a jihar Kano, Kano State Online Chapel ta sanar da fara sayar da fom din neman zama memba ga ’yan jarida da ke aiki musamman a fannin kafafen yada labarai na dijital da na intanet.

A wata sanarwa da Sakataren Kudi na kungiyar, Kwamared Kabiru Basiru Fulatan ya fitar, ya bayyana cewa ana sayar da Fom din ne kan naira ₦5,000 kacal. Kuma masu sha’awar shiga za su iya tuntubar Isyaku Ahmed a sakatariyar NUJ da ke Farm Center a Kano, daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma a kowace rana.

Kungiyar ta bukaci dukkan ’yan jarida da masu aiki a kafafen yada labarai na yanar gizo da su yi amfani da wannan dama don shiga cikin wannan kungiya mai inganci, wadda ke da burin hada kai da kuma bukasa harkar jarida a yanar gizo.

“Muna kira ga dukkan ’yan jarida da ma’aikatan kafafen yada labarai na yanar gizo da su yi amfani da wannan dama wajen shiga cikin wannan kungiya mai cike da tsare-tsare da kyawawan manufofi, wadda ta kuduri aniyar inganta harkar aikin jarida a Jihar Kano”.

 

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinsahabetsuperbetinmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet