Connect with us

Featured

A Shirye Muke Mu Tattauna Da Ƴan Bindiga – Gwamnatin Sokoto

Gwamnatin Jihar Sokoto ta jaddada kudurinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar, inda ta bayyana cewa a shirye take ta tattaunawa da ƴan bindigar da su ke da niyyar ajiye makamansu domin rungumar sulhu da zaman lafiya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Ba Gwamna Shawara Kan Harkokin Tsaro, Kanar Ahmed Usman (mai murabus), ya sanya wa hannu, inda aka jaddada cewa tattaunawa da sulhu abu ne mai matukar muhimmanci.

Sanarwar ta ce, “Yawancin rikice-rikicen da su ka faru a tarihi ba’a magance su ta hanyar amfani da karfi kawai ba, sai da aka yi tattaunawa mai ma’ana. Wannan ne ya sa gwamnatin jihar ke bude kofarta ga duk wani dan bindiga da ya nuna kwadayin mika wuya da komawa cikin al’umma cikin lumana.”

Har ila yau, gwamnatin ta bayyana godiyarta ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, hafsoshin tsaro, kwamandojin rundunoni da sauran jami’an tsaro wadanda ke kokarin bayar da kariya a yankin, kan sadaukarwar da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Mun gode da irin jajircewarsu. Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a bakin aiki, ya kuma bai wa iyalansu hakurin jure rashinsu,” in ji sanarwar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet