Connect with us

Featured

Jami’an Sa-Kai Sun Kashe Ɗanbokolo Da Wasu Manyan Yan ta’adda 6 – Gwamnatin Zamfara

An kashe Kachalla Yellow Danbokolo, babban ɗan bindiga kuma abokin dan ta’addar nan Bello Turji, tare da kwamandoji 6 da mayaƙa 182 a wani farmaki da jami’an Zamfara Community Protection Guards (CPG) suka kai a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Danbokolo, wanda daya ne daga cikin mutanen da suka addabi Arewacin Najeriya, an harbe shi ne a ƙafa, inda yayi ta zubar da jini kuma daga bisani jami’an tsaro suka kama shi suka sare kansa.

An ce yana shi ne ke da alhakin kai hare-hare masu yawa da sace mutane a jihohin Zamfara, Sokoto da ma wasu yankuna a Jamhuriyar Nijar. Wanda wasu ke ganin yana da ƙarfin soji fiye da Turji.

Mutuwarsa ta girgiza Bello Turji, wanda yanzu rahotanni ke cewa yana shirin tserewa zuwa Nijar ko Chadi saboda karancin sadarwa da tsananin farmakin jami’an tsaro.

Jami’an tsaro daga JTF, CPG, ’Yan sanda da DSS ne suka haɗu suka kai wa su Danbokolo hari bayan samun bayanan sirri cewa suna shirin kai farmaki.

Danbokolo daya ne daga cikin masu hannu a kisan Sarkin Gobir, Muhammad Bawa, da sauran hare-hare a Sokoto da Zamfara, musamman a Shinkafi.

Da yake tabbatar da mutuwar Kachalla Danbokolo, Mustapha Jafaru Kaura, Mai Ba Gwamna Dauda Lawal Shawara Kan Harkokin Watsa Labarai, ya bayyana cewa an kashe shahararren ɗan bindigar ne a wani ƙauye da ke cikin ƙaramar hukumar Shinkafi.

Ya ce: “Eh, gaskiya ne. An kashe Danbokolo a kusa da iyakar Najeriya da Chadi a wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka kai. Ina tabbatar da cewa wannan ci gaba ya raunana Bello Turji sosai.

Muna da yakinin cewa za a kama ko kuma a kashe Turji nan ba da jimawa ba. Dakarun Najeriya sun riga sun sha kansa, don haka yanzu kwanakin sa sun ƙare.”

 

 

 

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet