Featured
Nico Williams Ya Yi Watsi Da Barcelona Ya Sabunta Kwantaraginsa a Bilbao
Dan wasan gaba na ƙasar Spain, Nico Williams, ya sabunta kwantaraginsa a Athletic Bilbao wanda zai zaunar da shi a kulob din har nan da shekara goma.
Dan wasan mai shekara 22, wanda aka danganta shi da komawa Barcelona da kuma Bayern Munich na Jamus, yanzu dai ya tsawaita zamansa a Bilbao har zuwa 30 ga Yuni, 2035.
A baya dai yarjejeniyarsa za ta kare ne a shekarar 2027, amma yanzu an sabunta ta tare da ƙarin sharudda. Kulub din ya bayyana cewa kudin sakin dan wasan (release clause) da ake kyautata zaton ya kai €62m (£53m), yanzu ya karu da kashi 50%.
Wannan dai na zuwa ne bayan kungiyar Barcelona ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta dauki dan wasan a kakar cinikayyar yan wasa ta bana.
Bayan sabunta kwantaragin nasa a wannan rana ta Juma’a 04 ga Yuli 2025, Williams ya ce “Na bi shawarar da zuciyata ta bani, yanzu ina inda nake so, wato gida na.
