Featured
Atiku Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takara a Zaben 2027
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna sha’awar sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027.
Atiku, wanda ya tsaya takara da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a 2019, sannan ya kalubalanci shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2023, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin tsohon Minista, Idris Abdullahi.
Ya bayyana cewa sata da duk wata hanya ta cin hanci ba za su samu wurin zama ba a gwamnati ƙarƙashin jagorancinsa.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce, “A yanzu ya isa haka.”
Ya ƙara da cewa: “Zamu hukunta duk wanda ya ce zai saci ko ya bullo da wata hanyar cin hanci da rashawa. Zamu yaƙe shi, wallahi. Ya isa haka! Kowace ƙasa tana cigaba, amma Najeriya kullum wasu mutane kalilan sun hana mata ci gaba.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa muka tabbatar cewa tsarin shugabancinmu na wucin gadi ya ƙunshi mutane masu gaskiya da amana. Kuma daga nan ne za a fahimci irin salon shugabancin da muke shirin kawo wa.”
