Featured
An Yi Wa Maganar Kashim Shettima Mummunar Fahimta, Ba Tada Alaka Da Dakatar Da Fubara – Fadar Shugaban Kasa
Fadar Shugaban Kasa ta karyata rade-radin da ke cewa kalaman da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yi a wajen kaddamar da wani littafi a Abuja na da nasaba da abin da ke faruwa a Jihar Ribas tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa (Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), Stanley Nkwocha, ya fitar a ranar Juma’a 11 ga Yuli, ya bayyana yadda wasu kafafen yada labarai suka fassara kalaman Shettima da cewa hakan “kuskurene mai girma” da kuma “barazana ga hadin kan kasa.”
Shettima ya yi jawabi ne a wajen gabatar da littafin “OPL 245: The Inside Story of the $1.3 Billion Oil Block,” wanda tsohon Antoni Janar na Tarayya, Mohammed Bello Adoke, SAN, ya rubuta, a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja ranar Alhamis 10 ga Yuli, 2025.
A cewar Nkwocha, Mataimakin Shugaban Kasa ya yi bayani kan wani lamari da ya faru a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, inda aka yi yunkurin sauke shi daga mukaminsa na Gwamnan Jihar Borno a lokacin da Boko Haram ke kara ta’azzara a yankin Arewa maso Gabas.
Ya kuma bayyana cewa kalaman Shettima na nuna godiya ne ga rawar da Adoke ya taka a lokacin da yake Antoni Janar na kasa, ba wai yana mayar da martani ba ne kan siyasar da ke gudana a yanzu.
“Wasu kafafen yada labarai sun karkatar da kalaman Mataimakin Shugaban Kasa ta hanyar yin amfani da su wajen gina tatsuniya da suka danganta su da matakin da aka dauka a Jihar Ribas, da suka hada da ayyana dokar ta-baci da kuma dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara daga mukaminsa da Shugaba Tinubu ya yi.
“Muna so mu fayyace cewa kalaman Shettima ya yi su ne dangane da abubuwan da suka faru a lokacin gwamnatin Jonathan.”
Tun da farko dai wasu jaridu sun bayyana kalaman na Kashim a matsayin wani dukan sari-ka-noƙe game da matakin Shugaba Tinubu na dakatar da Gwamna Fubara.
Nkwocha ya ce irin wannan fassara ba ta da tushe kuma tana jefa mutane cikin rudani, domin ba a tsige Gwamna Fubara daga mukaminsa ba.
“Don kawar da shakku, Shugaba Tinubu bai tsige Gwamna Fubara daga ofis ba. Matakin da aka dauka na dakatarwa ne kawai, ba tsigewa ba. Wannan yana cikin jerin matakan da aka dauka don shawo kan rikicin siyasa da kuma barazanar tsaro da ta kunno kai a Jihar Ribas a lokacin.
“Wannan ya biyo bayan halin da ake ciki na rusa majalisar dokokin jihar da kuma barazanar tsige gwamnan da wasu ‘yan majalisa da ke cikin rikici da shi suka yi,” in ji shi.
