Featured
Gwamnoni Sun Ƙarɓi Naira Triliyan 4.5 Na Kuɗin Ƙananan Hukumomi Shekara Guda Bayan Hukuncin Kotun Koli
Shekara guda bayan Kotun Koli ta yi hukunci cewa a rika ba wa kananan hukumomi 774 na Najeriya kuɗinsu kai tsaye daga Asusun Tarayya, Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da tura kuɗin ta hannun gwamnatocin jihohi.
Rahoton da jaridar The PUNCH ta fitar ya nuna cewa gwamnonin jihohi sun ci gaba da rike ikon sarrafa kuɗin kananan hukumomi da suka kai Naira tiriliyan 4.5, duk da hukuncin ya bukaci a rika tura kuɗin kai tsaye.
A ranar 11 ga Yuli, 2024, Kotun Koli ta yanke hukunci cewa tura kudin Ƙananan hukumomi ta hannun gwamnoni abu ne da ya saɓawa ka’ida, kuma dole ne a canza tsarin. Daga nan ne Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin da zai tabbatar da aiwatar da hukuncin, tare da umartar CBN da ta bude asusun kowacce karamar hukuma.
Sai dai bayan shekara guda, rahotanni sun tabbatar cewa ba a aiwatar da tsarin ba. Ana ci gaba da tura kudaden ta jihohi, saboda tsaiko daga CBN, gwamnoni, shugabannin LG da wasu hukumomi.
