Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Talata A Matsayin Ranar Hutu A Fadin Ƙasar Domin girmamawa Ga Buhari
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata, 15 ga Yuli, 2025 a matsayin hutu a fadin kasar domin girmama marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, bayan amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wannan sanarwa na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na kwana bakwai na zaman makoki da Shugaba Tinubu ya ayyana domin karrama rayuwar marigayi Buhari.
Buhari ya rasu yana da shekara 82 a wani asibiti da ke birnin London.
A wata sanarwa da Magatakardar Dindindin na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani, ta fitar, Tunji-Ojo ya bayyana Buhari a matsayin shugaba wanda ya yi wa Najeriya hidima da ƙwazo da amana.
Ya ƙara da cewa hutun kasa an shirya shi ne domin bai wa ‘yan Najeriya damar yin tunani a kan gudunmuwar da marigayin ya bayar wajen gina dimokuraɗiyya da cigaban ƙasa.
