Connect with us

Featured

Cin Hanci Bai Samu Matsuguni A Mulkin Buhari Ba – Malami

Tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na Najeriya na baya bayan nan, Abubakar Malami, ya mayar da martani kan masu suka ga kokarin yaki da cin hanci da gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi.

Yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Arise News da yammacin Talata 15 ga Yuli 2025, Malami ya bayyana cewa marigayi shugaba Buhari bai taba bari cin hanci ya yi katutu a lokacin mulkinsa ba.

A cewarsa: “A lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, cin hanci bai samu gindin zama ba ko kadan.”

Ya kara da cewa gwamnati ta samu nasarar hukunta dubban mutane da suka aikata manyan laifukan cin hanci da rashawa a lokacin mulkin Buhari.

Tsohon Antoni Janar ya kuma bayyana cewa Najeriya ta kwato fiye da dala biliyan biyu da aka wawure daga baitul malin kasa a lokacin gwamnatin Buhari.

Ya ce gwamnatin Buhari ta fara aiwatar da wasu muhimman gyare-gyare irin su Asusun Bai Daya na Kasa (TSA) da Lambar Tantance Banki (BVN) domin dakile asarar kudade da suka saba faruwa a baya.

“Ya kirkiro da Asusun Bai Daya, wanda ya bai wa gwamnati cikakken iko da gani a duk inda kudi ke shiga ko fita,” in ji shi.

A matakin kasa da kasa kuwa, Malami ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta samu yabo daga kungiyoyi kamar Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) wadda ta ayyana shi a matsayin gwarzon yaki da cin hanci a nahiyar, da kuma Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da Miyagun Kwayoyi da Laifuka (UNODC).

A halin yanzu, ana ci gaba da bayyana marigayi Shugaba Buhari a matsayin daya daga cikin shugabannin Najeriya da suka fi kokari wajen yakar cin hanci.

 

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet