Connect with us

Featured

Ƴan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11 Bisa Zargin Kashe Abokan Karatunsu Biyu a Kano

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kama ɗalibai 11 na Makarantar Sakandare ta Kwana ta Gwamnati da ke Bichi, bisa zargin hannu a kisan wasu ɗalibai biyu a makarantar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan ga jaridar PUNCH Online a ranar Alhamis 17 gà Yuli, 2025.

A cewarsa, an kama ɗaliban ne domin gudanar da bincike da gano yadda kowane ɗalibi ke da hannu a cikin lamarin.

A cewarsa, an kama ɗaliban ne domin gudanar da bincike da gano yadda kowane ɗalibi ke da hannu a cikin lamarin.

Ya ce: “An kama ɗalibai 11 dangane da wannan lamari, kuma bincike na ci gaba da gudana don gano matsayinsu a cikin lamarin.”

SP Kiyawa ya ƙara da cewa rundunar ‘yan sanda za ta yi duk mai yiwuwa wajen gano gaskiyar lamarin da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

A ranar Laraba 16 ga Yuli, ne Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar ɗaliban.

Wannan umarni ya fito ne ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta Jihar, Bashir Bappa Mohammad, yayin ziyarar sa zuwa makarantar.

Ana zargin cewa marigayan — Hamza Idris Tofawa da Umar Yusuf Dungurawa — sun mutu ne sakamakon hari da wasu ɗalibai suka kai musu da wani irin ƙarfe na gida da aka fi sani da “Gwale-Gwale”.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet