Featured
Tinubu Ya Canza Sunan Jami’ar Maiduguri Zuwa Muhammadu Buhari
Gwamnatin Tarayya ta sanar da sauya sunan Jami’ar Maiduguri, inda yanzu ta koma Jami’ar Muhammadu Buhari, domin girmamawa ga tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari.
Sanarwar hakan ta fito ne daga taron na musamman na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) da ke gudana a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a yau Alhamis17 ga Yuli, 2025.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana haka, inda ya ce sauya sunan jami’ar na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin girmama abubuwan da marigayin shugaban ƙasa ya tsaya a kansu da irin gudunmawar da ya bayar ga ƙasar nan.
Marigayi Muhammadu Buhari dai ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti da ke Landan, kuma an binne shi a Daura, Jihar Katsina, a ranar Talata.
