Connect with us

Featured

Likitoci Za Su Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Najeriya – NMA

Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta sanar da shirin fara yajin aiki a faɗin ƙasa baki ɗaya daga ranar Alhamis 24 ga Yuli, idan har gwamnatin tarayya ta gaza cika bukatunsu kafin ƙarewar wa’adin kwanaki 21 da suka bayar wanda zai ƙare a ranar 23 ga watan Yuli, 2025.

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Bala Audu, ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi 20 ga Yuli, 2025. Ya ce ƙungiyar ta NMA za ta dauki matakin karshe idan gwamnati ta ci gaba da yin shiru game da matsalolin da suka gabatar.

Ya ce buƙatun da ƙungiyar ta NMA ke nema suna da matuƙar muhimmanci wajen ceto tsarin kiwon lafiya a Najeriya, da kuma kare walwalar likitoci a fadin ƙasar.

NMA ta bayyana cewa a ranar 2 ga Yuli ne ta fitar da wa’adin kwanaki 21 a matsayin martani ga wata sabuwar takarda daga Hukumar Albashi da Albarkatu (NSIWC) wadda ta yi sauyi a wasu kudaden alawus-alawus na likitoci da ma’aikatan hakora a ma’aikatar gwamnatin tarayya – sauyin da suka ce ya sabawa yarjejeniyar da aka cimma a baya.

Farfesa Audu ya ce, “Mun bayyana matsayar mu karara. Idan gwamnati ta gaza cika buƙatun mu kafin 23 ga Yuli, babu abin da ya rage mana illa mu tafi yajin aiki.”

Ya kara da cewa sabuwar takardar da NSIWC ta fitar tana dauke da abubuwan da ba a tattauna ba da ƙungiyar, kuma hakan ya ci gaba da illata halin da likitoci ke ciki.

“Mun ƙi amincewa da takardar gaba ɗaya. Duk wani sabon umarni da ya shafi mambobinmu ya zama tilas sai an yi shawara da mu a baya, ba tare da an tilasta mana ba,” in ji shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet