Featured
WAEC Ta Ƙaryata Jita-jitar Soke Jarrabawar SSCE Ta 2025
Hukumar shirya jarrabawa ta Afrika ta Yamma (WAEC) ta karyata rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an soke jarrabawar WASSCE ta shekarar 2025 da aka kammala a baya bayan nan.
A cikin wata sanarwa da mai rikon mukamin Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na WAEC, Moyosola Adesina, ya fitar a ranar Lahadi 20 ga Yuli, hukumar ta bayyana cewa sanarwar da ke yawo ba daga ukumar ta fito ba, don haka tana tabbatarwa jama’a ba gaskiya ba ce.
Sanarwar ta ce: “WAEC ta lura da wata sanarwa da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa wai an soke dukkan jarrabawar WASSCE ta 2025 saboda yawaitar magudin jarrabawa, fitar tambayoyi kafin lokaci, da yada kayan jarrabawa ta hanyar fasaha.”
“Muna son bayyana cewa wannan rahoto karya ne kuma ba ya da tushe. WAEC ba ta soke jarrabawar ba, kuma babu wani shiri na yin hakan.”
Hukumar ta kara da cewa tuni masu duba takardun jarrabawar sun kammala aikin su, kuma za a fitar da sakamakon jarrabawar a ranar Litinin, 4 ga watan Agusta, 2025 ko kafin ranar.
WAEC ta bayyana cewa duk wani bayani matukar daga gareta yake, tana fitar da shi ne ta hanyar shafinta na hukuma da kuma kafafen yada labarai da aka tantance a fadin kasar.
WAEC ta bukaci dalibai da iyaye da sauran jama’a su yi watsi da wannan jita-jita, tana mai cewa makircin ne na masu neman bata sunanta da kuma tada hankalin jama’a.
