Connect with us

Featured

Najeriya Tana Asarar Naira Tiriliyan 17.9 Duk Shekara Sakamakon Ciwon Hanta – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Najeriya na asarar kimanin Naira tiriliyan 13.3 zuwa 17.9 duk shekara ta fuskar kai tsaye da kuma wadanda ba kai tsaye ba, saboda cutar hanta

Haka kuma, gwamnati ta ce mutane 4,252 na mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon daji na hanta da ke faruwa saboda rashin maganin hepatitis.

Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Pate, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin 28 ga Yuli, domin bikin ranar Ciwon Hanta ta duniya.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), hepatitis cuta ce da kehaddasa kumburin hanta wacce ke da hanyoyi daban-daban na yaduwa, kuma na iya kaiwa ga lalacewar hanta da ciwon daji — wasu lokuta ma har a rasa rai.

Akwai nau’uka biyar na cutar hepatitis: A, B, C, D da E. Kowanne na iya haddasa ciwon hanta, sai dai hanyoyin yaduwa, tsanani, yanki da ya fi shafar cutar, da hanyoyin kariya suna bambanta.

Farfesa Pate, wanda Daraktan Lafiya ta Jama’a a ma’aikatar, Dakta Godwin Ntadom, ya wakilta, ya bayyana cewa Najeriya na da matsanancin nauyin cutar hepatitis, inda mutane sama da miliyan 20 ke dauke da ita.

Ya ce: “Najeriya na da fiye da mutane miliyan 20 da ke dauke da cutar hepatitis B da C — miliyan 18.2 na dauke da Hepatitis B, yayin da miliyan 2.5 ke dauke da Hepatitis C.

“Fiye da kashi 8.1 na al’ummar kasar na dauke da Hepatitis B, kuma duk da akwai rigakafi da magani, fiye da kashi 90 cikin 100 daga cikinsu ba a gano su ba, kuma suna ci gaba da yada cutar ba tare da sani ba — har ma ga yara.

“A mafi yawan lokuta, alamomin cutar kamar zazzaɓi, gajiya da rashin lafiya ana daukarsu a matsayin zazzabin cizon sauro. Sakamakon haka, ana shan magungunan gida yayin da cutar ke ci gaba da lalata hanta har ta kai ga gazawarta ko kuma ciwon daji.

“A kowace shekara, mutane 4,252 ke mutuwa sakamakon ciwon daji na hanta da ke faruwa saboda hepatitis da ba a yi masa magani ba.

“Kudin da cutar ke janyo wa tattalin arzikin kasa ya kai tsakanin Naira tiriliyan 13.3 zuwa 17.9 a kowace shekara.”

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet