Featured
Jirgin Ruwa Ɗauke Da Ƴan Ci-Rani Ya Yi Ajalin Mutane 76 Yayin Da Ya Nutse Kusa Da Yemen
Aƙalla mutane 76 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka bace bayan da wani jirgin ruwa da ke ɗauke da mafi yawan ‘yan hijira daga ƙasar Habasha ya kife a gabar ruwan Yemen, kamar yadda jami’an tsaronsu ka bayyanawa AFP a ranar Litinin 04 ga Agusta, 2025.
Jami’an tsaro na Yemen sun ce an gano gawarwaki 76, yayin da aka ceto mutane 32 daga cikin jirgin da ya nutse a Tekun Gulf of Aden. Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM) ta ce jimillar fasinjojin da ke cikin jirgin su 157 ne.
Hatsarin ya faru ne a gabar gundumar Abyan da ke kudancin Yemen, wadda ta shahara da karɓar jiragen ruwa da ke ɗauko ‘yan gudun hijira daga Afirka da ke ƙoƙarin isa ƙasashen masu arziki a yankin Gulf.
Wasu daga cikin waɗanda aka ceto an kaisu birnin Aden na Yemen, kusa da Abyan, kamar yadda wani jami’in tsaro ya bayyana.
A baya dai, hukumar IOM ta ce aƙalla mutane 68 ne suka mutu a hadarin.
Shugaban hukumar IOM na ƙasar Yemen, Abdusattor Esoev, ya shaida wa AFP cewa, “ba a san halin da waɗanda suka bace ke ciki ba har yanzu.”
Duk da yaƙin basasa da ya addabi Yemen tun 2014, ƙasar da ke cikin matsanancin talauci ta ci gaba da kasancewa muhimmin hanyar da ‘yan hijira ke bi, musamman daga ƙasar Habasha wadda ke fama da rikicin ƙabilanci.
Duk shekara, dubban mutane ne ke ƙoƙarin bin hanyar da ake kira “Eastern Route” daga Djibouti zuwa Yemen ta Tekun Red Sea, da fatan isa ƙasashen Gulf masu arzikin man fetur, kamar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Hukumar IOM ta ƙididdige cewa a shekarar da ta gabata kaɗai, mutane 558 ne suka mutu a hanyar Tekun Red Sea, inda 462 daga ciki suka mutu sakamakon haɗurran jirgin ruwa.
A watan da ya gabata, aƙalla mutane takwas ne suka mutu bayan da masu safarar mutane suka tilasta wa ‘yan hijira su fice daga cikin jirgin ruwa a cikin Tekun Red Sea, kamar yadda hukumar IOM ta bayyana.
Jirgin da ya nutse a gabar Abyan ya ƙunshi mafi yawancin ‘yan hijira daga ƙasar Habasha, in ji hukumar tsaron Abyan da kuma wata majiya daga IOM.
