Connect with us

Featured

Gwamnatin Jihar Delta Za Ta Ƙwace Baburan Haya Ko Keke Napep Ɗin Da Masu Su Basu Biya Harajin N7,500 Ba

Gwamnatin Jihar Delta ta yi barazanar kwace babura na haya (Keke Napep) da babura, idan masu su suka kasa biyan kuɗin da aka kayyade na Naira 7,500 domin samun kati na direba, rigar aiki (apron), tambari da kuma sitika cikin makonni biyu masu zuwa.

Wannan gargadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai kuma Mukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta jihar, Harold Ojji, ya fitar a garin Warri ranar Talata 05 ga Agusta.

Sanarwar ta ce: “An sanar da jama’a, musamman masu babura (Okada) da kekuna (Keke Napep), cewa Gwamnatin Jihar Delta ta ƙara ba su ƙarin kwanaki 14 domin su mallaki rigar aiki, sitika da kati na direba kamar yadda gwamnatin ke aiwatar da shirin tantance masu ababen hawa domin tsaro.

“Saboda haka, duk masu babura da kekuna na haya an umurce su da su saya rigar aiki, tambari, sitika da katin direba a farashin da gwamnati ta rage – Naira 7,500 – daga ofisoshin ƙungiyar masu babura da kekuna na haya (Commercial Motorcycle and Tricycles Operators’ Association) a faɗin jihar.”

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Za a kwace babura da kekuna da suka gaza bin wannan umarni daga hannun masu su bayan cikar kwanaki 14 da aka bayar. Kwacen zai gudana ne ta hannun Ma’aikatar Sufuri (Vehicle Inspection Officers), jami’an tsaro, da Task Force na ƙungiyar COMTOA daga ranar 18 ga watan Agusta, 2025.”

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet