Connect with us

Featured

Jami’an NSCDC Sun Kama Wani Babban Mai Safarar Miyagun Kwayoyi a Kano

Jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) reshen Jihar Kano sun kama wasu da ake zargi da aikata laifuka biyu daban-daban — safarar miyagun kwayoyi da kuma fasa gidan mutane da sata.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Abdullahi, ya fitar a ranar Laraba 06 ga Agusta, wadda aka rabawa manema labarai.

A cewar sanarwar: “Jami’an NSCDC sun sake samun gagarumar nasara wajen yaƙi da miyagun laifuka, inda suka kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a wasu samamen daban-daban.”

“Na farko, jami’an NSCDC sun cafke wani da ake zargi da safarar kwaya mai suna Basiru Ahmed, mai shekaru 42, a unguwar Salanta dake karamar hukumar Gwale, yayin da aka same shi da wasu sinadarai da ake zargin tabar wiwi ce (Cannabis sativa).”

Sanarwar ta kara da cewa an kama wanda ake zargin ne bisa bayanan sirri masu inganci, kuma an same shi a yayin da yake sayar da miyagun kwayoyin ga mutanen unguwar.

“An kama wanda ake zargin da fiye da fakiti 106 na tabar wiwi, kuma an mika shi ga hukumar NDLEA ta jihar Kano domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakin doka da ya dace.”

A wani lamari makamancin haka, wani matashi mai suna Muhammad Abbas, dan shekara 22, ya shiga hannun jami’ai a unguwar Gurungawa dake karamar hukumar Kumbotso.

An kama shi ne bisa zargin fasa gidan mutane tare da satar kayayyakin da kudinsu ya kai dubban naira.

“Wanda ake zargin ya dade yana cikin jerin sunayen da jami’an tsaro ke sa ido a kansu. An kama shi ne yayin wani sintiri na musamman da aka kaddamar domin dakile sata da wasu laifuka a yankin,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa dukkan wadanda ake zargin za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Hukumar ta kuma bukaci al’umma da su ci gaba da kasancewa masu lura da abin da ke faruwa a muhallinsu tare da bayar da bayanai cikin lokaci domin a ci gaba da kawar da miyagun mutane daga cikin al’umma.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet