Connect with us

Featured

Ƙarancin Abinci Ya Tilastawa Mutane Cin Abincin Dabbobi a Sudan – Majalisar Ɗinkin Duniya

A Sudan, musamman a birnin El Fasher, rahotanni sun nuna cewa yunwa na ƙara tsananta har ta kai talakawa sun fara cin abincin dabbobi, yayin da mata da ‘yan mata ke fuskantar abin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kira “gaggawar jinsi” a ƙasar, kamar yadda jami’i a majalisar ɗinkin duniya ya bayyana a ranar Alhamis 07 ga Agusta, 2025.

Ofishin Tsare-Tsaren Ayyukan Jin Kai na MDD (OCHA) ya yi gargadin cewa halin da ake ciki na tabarbarewa yana ƙara jefa rayukan fararen hula cikin haɗari.

Mai magana da yawun mataimakin Sakatare-Janar na MDD, Farhan Haq, ne ya bayyana hakan a hedikwatar MDD a New York cewa tsadar rayuwa a El Fasher ta kai matuka, a cewarsa tsadar kaya, tare da killacewar garin da kuma rashin isar da agaji ta hanya tsawon fiye da shekara guda, ya sa dubban mutane na fuskantar yunwa mai tsanani.

Daraktan Ayyuka da Yabo na OCHA, Edem Wosornu, wadda ke ziyara a Sudan, ta ce wahalar ta yi tsanani ƙwarai, inda mutane ke makale, wasu an raba su da muhallansu, wasu kuma na komawa su tarar da garuruwansu a rushe. Ta bukaci a ba da damar shiga ba tare da tangarda ba da kuma gaggawar isar da taimako ga masu fama da ƙuncin rayuwa.

Haka nan, hukumar UN Women ta yi gargadi cewa wannan matsala ta zama “gaggawar jinsi”, inda Salvator Nkurunziza, wakilin hukumar a Sudan, ya bayyana cewa mata da ‘yan mata da aka raba da muhallansu na iya fuskantar haɗarin cin zarafi da lalata, musamman a lokacin rabon agaji inda babu isassun matakan kariya a wasu wurare.

 

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet