Connect with us

Featured

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon watanni uku domin bai wa kwamiti damar gudanar da bincike kan zarge-zargen aikata ba daidai ba, cin zarafi da kuma karkatar da kudaden gwamnati.

An yanke wannan hukunci ne bayan gabatar da rahoton wucin-gadi na Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na Jama’a da shugaban masu rinjaye a majalisar, Hussaini Lawan Cediyar Yangurasa, ya jagoranta a zaman majalisa na ranar Laraba 13 ga August 2025.

Majalisar ta umurci Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu ta tura mataimakin shugaban ƙaramar hukumar ya karɓi ragamar mulki a matsayin mai rikon kwarya har sai an kammala bincike.

Wasu daga cikin zarge-zargen da aka yi wa shugaban sun haɗa da: ƙirƙirar rigima da rashin jituwa tsakanin shugabannin siyasa da kansiloli, raba kayan gwamnati kawai ga magoya bayansa, rarraba takardun shiga makarantar Dangote da taki na GES da na gwamnati ta hanyar fifita wasu, da sayar da taki sama da farashin ₦20,000 da gwamnati ta amince, ba tare da sanin kansiloli ba. Haka kuma an zarge shi da rashin gaskiya wajen kula da kuɗaɗen haraji daga kasuwanni, da wasu kudaden shiga, sayarwa da rarraba rumfunan kasuwa da shagunan da aka gina ba tare da sanin majalisar ƙaramar hukumar ba, tozarci da raina dattawan jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki, tare da yin amfani da kuɗaɗen ƙaramar hukuma ba bisa ƙa’ida ba.

Kwamitin ya gana da ɓangarorin biyu a ranar Talata, 11 ga Agusta, inda shugaban ya ƙaryata wasu daga cikin zarge-zargen, amma ya amince cewa ya ƙara farashin taki da ₦2,000 fiye da farashin ₦20,000 da gwamnati ta tsara.

Kwamitin, bisa ga Sashe na 55(1-6) na Dokar Kananan Hukumomi ta 2006, ya tabbatar da dakatar da Yau domin gudanar da cikakken bincike. Haka kuma kwamitin ya umurci a kawo dukkanin bayanan kuɗi da na gudanarwa na ƙaramar hukumar cikin kwanaki bakwai.

A zaman ranar Laraba 13 August, wanda Kakakin Majalisar, Ismail Falgore, ya jagoranta, majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet