Connect with us

Featured

Saurin Hannu: Majalisar dokokin Kano ta buƙaci jam’iyyar APC ta hukunta Alasan Ado Doguwa

Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci shugabancin jam’iyyar APC tun daga matakin ƙasa har zuwa jiha da ya hukunta shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya kuma ɗan majalisa mai wakiltar Ƙananna hukumomin Doguwa da Tudun Wada Alasan Ado Doguwa, a kan ɗabi’unsa da majalisar ta kira da munana.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da shugaban masu rinjaye na majalisar Labaran Abdul Madari, ya fitar mai ɗauke da sa hannun Sakataren yaɗa Labaran majalisar Uba Abdullahi.

Sanarwar ta kuma ce, irin wannan hali na iya kawo cikas ga ci gaban Jam’iyyar ta APC.

Haka kuma sanarwar ta yi Allah-wadai da halin rashin da’a na shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai kan abin da ya faru tsakaninsa da mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen baɗi Murtala Sule Garo.

Ta cikin sanarwar dai, majalisar ta ƙara da cewa ɗan majalisar ya sake aikata irin wannan rashin kirki ga tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi da Injiniya Muhd ​​Ali Wudil dan majalisar wakilai mai wakiltar Garko da Wudil a majalisar tarayya da kuma mai magana da yawun jam’iyyar APC na jiha Ahmed Aruwa.

Majalisar dokokin ta jihar Kano, ta kuma jaddada matsayin ta na tabbatar da nasarar jam’iyyar APC mai mulki a dukkan matakai a zaɓen baɗi da ke tafe a cewar sanarwar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet