Connect with us

Labarai

Ƴar Najeriya ta zama Birgediya Janar ta sojin Amurka

Wata sojar Amurka ƴar asalin Najeriya Amanda Azubuike, ta samu ƙarin girma daga mukamin Laftanar Kanal zuwa Birgediya Janar. 

Amanda Azubuike, wadda dangin ta zke da alaƙa da Najeriya, ta samu sabon muƙamin ne yayin wani bikin da aka gudanar na wani rukunin sojoji da ke Fort Knox dake Kentucky, a ƙasar ta Amurka.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, wani babban kwamanda na rundunar sojin Amurka Janar James Rainey, ya ce bisa Irin jagorancin Azubuike da ta yi kowa da ya kasance a karkashin ta ya gamsu da salon jagorancin ta.”

Azubuike, Yar kasar Amurka, iyayen ta ne, ‘Yan Najeriya, Kuma suka haife ta a birnin Landan na kasar Ingila.

Tun a Shekarar 1994 ta shiga kwalejin horas da Jami’an Jiragen Sama na Sojoji.

Kafin ta koma aikin Soja a matsayin jami’ar hulda da jama’a, ta yi aiki a bangaren sufurin jiragen sama na tsawon shekaru 11.

Amanda Azubuike ta taba rike mukamin Mai bada shawara ga babban hafsan sojoji, a ofishin sakataren tsaro.

A halin yanzu, dai ta kasance mataimakiyar kwamanda a Rundunar Sojojin Amurka.

A baya ta rike mukaman Daraktar Hulda da Jama’a a shiyyar Washington da Kuma shugabar sashen Hulda da Jama’a a Rundunar Kudancin Amurka wato yankin Fort Lauderdale.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet