Connect with us

Featured

Dalibin Likitanci Ya Kashe Kansa Bayan Ya Faɗi Jarabawa Sau Biyu

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife, Jihar Osun, ta tabbatar da mutuwar wani ɗalibin likitanci na mataki na biyu, Ajibola Ibitayo, wanda ya kashe kansa.

A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Mista Abiodun Olarewaju, ya fitar a ranar Alhamis 14 Agusta, ya bayyana cewa ɗalibin mai lambar shiga DEN/2021/023 ya kashe kansa bayan ya fadi jarabawarsa, wanda hakan zai tilasta masa maimaita ajin mataki na biyu karo na biyu.

Olarewaju ya ce sakamakon jarabawarsu na zangon da ya gabata an fitar da shi a ranar Laraba 13 ga Agusta, kuma sakamakon ya nuna cewa dole ne Ibitayo ya sake maimaita mataki na biyu na likitanci a wannan shekarar.

“Tuni dai yana maimaita wannan matakin a shekarar karatu ta baya,” in ji shi.

Rahotanni sun nuna cewa ɗalibin, wanda mahaifinsa likita ne, ya kashe kansa ta hanyar yi wa kansa allura a gidansu da ke garin Ejigbo, Jihar Osun.

Shugaban jami’ar, Farfesa Simeon Bamire, ya bayyana bakin cikinsa, inda ya roki iyaye da masu kula da yara su koyar da su fahimtar cewa koma-baya na ɗan lokaci a tafiyar neman nasara wani ɓangare ne na rayuwa, ba ƙarshen ta ba ne.

Bamire ya kuma shawarci ɗalibai da matasa da su kalli gazawa a matsayin dama ta sake tsara hanyar da za ta kai su ga nasara da manyan ƙwarewa.

Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya ba iyaye, ‘yan uwa, Kwalejin Kimiyyar Lafiya da al’ummar jami’ar haƙurin jure wannan babban rashi.

 

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet