Connect with us

Featured

Bai Kamata Jonathan Ya Tsaya Takara a 2027 Ba — Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shawarci tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan da kada ya tsaya takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2027, inda ya yi gargadin cewa siyasar Najeriya ta yanzu ta bambanta da yadda ta ke a baya.

Da yake magana a shirin Sunday Politics na Channels Television, Sani ya ce jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wadda a ita Jonathan ya yi nasarar lashe zaɓe a 2011, yanzu ta rushe ba ta da ƙarfi.

“Kowane lokaci idan zaɓe ya zo, ana kawo sunan Jonathan. Amma ko da yake yana da ‘yanci ya tsaya, shawarar da zan bashi ita ce kada ya yi hakan. Dalili kuwa shi ne PDP da ya sani a baya, ba ita ce PDP a yanzu ba.

PDP ta Kudu maso Yamma tana mara wa shugaban ƙasa baya. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar suna cikin wannan sabuwar haɗaka. Saboda haka ba ita ce jam’iyyar da ya sani ba, don haka bai kamata ya ɓata lokacinsa ba,” a cewar Sani.

Sani ya kuma yi watsi da ƙarfin sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa, yana mai cewa babu zurfin ra’ayi ko bambancin akida tsakaninsu da tafarkin siyasar Shugaba Bola Tinubu.

“Muna cikin dimokuraɗiyya, kuma a tsarin dimokuraɗiyya akwai damar kafa jam’iyyar adawa domin bayar da wata madogara. Amma idan manufarsu kawai ita ce su kifar da Tinubu ba tare da suna da wani tsari daban na mulki ko tafiyar siyasa ba, to babu ajandar su.

Mutanen da ke cikin wannan haɗaka a yau, ba su da bambanci a ra’ayi da manufofin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa. Ba kamar yadda za ka ce Marxist da Capitalist ne ko Neo-Liberal da Conservative ba.

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet