Featured
Najeriya Na Kashe Dala Biliyan 10 Duk Shekara Wajen Shigo da Abinci — Ministan Noma
Ministan Noma Abubakar Kyari, ya bayyana cewa Najeriya na kashe kusan dala biliyan 10 a duk shekara wajen shigo da kayan abinci daga waje, ciki har da alkama da kifi.
Kyari ya bayyana haka ne a ranar Talata 19 ga Agusta a birnin Legas, yayin taron First Bank of Nigeria Ltd. 2025 Agric and Export Expo.
Ministan, wanda mai ba shi shawara na musamman, Mista Ibrahim Alkali, ya wakilta, ya nuna damuwa kan yadda ake ta ƙara dogaro da shigo da abinci daga waje, inda ya jaddada buƙatar ƙarin saka jari a harkar noma domin ƙarfafa samar da abinci a cikin gida tare da haɓaka fitar da kayayyakin noma zuwa ƙasashen waje.
“Najeriya na kashe fiye da dala biliyan 10 a kowace shekara wajen shigo da kayan abinci irin su alkama, shinkafa, sikari, kifi, har ma da jan tumatir da aka nika.
Noma na bayar da kashi 35 cikin 100 na GDP ɗinmu, kuma kashi 35 cikin 100 na ma’aikatanmu suna harkar noma.
Muna da fili mai noma har hekta miliyan 85, tare da matasa sama da kashi 70 cikin 100 da shekarunsu ba su kai 30 ba. Amma duk da haka, Najeriya na bayar da ƙasa da kashi 0.5 cikin 100 na fitar da kayan noma a duniya.
A halin yanzu, ƙasar na samun ƙasa da dala miliyan 400 daga fitar da kayan noma. Idan muna son gina tattalin arzikin da bai ta’allaka da mai ba, dole mu sake tunanin yadda muke saka jari a noma,” in ji shi.
Kyari ya sake jaddada aniyar gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu wajen cimma ’yancin kai a fannin abinci, inda ya ce akwai gaggawar buƙatar ƙara saka jari a harkar noma.
— NAN
