Connect with us

Featured

Gwamnatin Katsina Ta Tabbatar da Mutuwar Mutane 32 a Harin da Aka Kai Masallaci

Mutane 32 ne aka tabbatar sun mutu a harin da ’yan bindiga suka kai da safiyar Talata a masallacin unguwar Mantau, karamar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.

’Yan bindigar sun afka masallacin ne misalin ƙarfe 5:00 na safe lokacin da jama’a ke sallar Asuba, inda suka fara harbi a matsayin ramuwar gayya bayan al’ummar wani kauye sun yi musu kwanton bauna kwanaki kadan da suka wuce.

Da farko rahotanni sun ce mutum 13 ne suka rasu, amma gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa mutum 32 ne suka mutu, yayin da wasu kuma aka sace. An ce rundunar sojin sama ta kai hari ta sama, inda aka ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace.

Gwamna Dikko Radda, wanda ke kan jinya, ya aika da tawaga ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnati, Abdullahi Faskari, domin yin ta’aziyya ga al’umma.

Faskari ya bayyana harin a matsayin “abin takaici mai zafi,” tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen fatattakar ’yan bindiga.

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Dr. Nasir Mu’azu, ya ce harin ya biyo bayan kwanton bauna da al’ummar Ruwan Sanyi suka yi wa ’yan bindiga, inda suka kashe da dama, suka kwace makamai da babura.

Ya ce an tura ƙarin sojoji da ’yan sanda yayin da ake ci gaba da aiki ta sama da ƙasa don kamo masu laifin.

Gwamnati ta ce tuni ta fara bai wa iyalan mamatan tallafi, tare da ci gaba da aikin tantance barnar da aka yi.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet