Featured
Gwamnan Neja Ya Rusa Majalisar Zartarwar Jihar
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya rusa majalisar zartarwarsa baki ɗaya. Sai dai ya sake tabbatar da Sakataren Gwamnatin Jihar, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin jihar da Mataimakinsa da wasu manyan jami’ai a mukamansu.
Sanarwar rushewar ta fito ne daga Mai Magana da Yawun Gwamnan, Bologi Ibrahim, a yayin taron Majalisar Zartarwa da aka gudanar a dakin taro na Fadar Gwamnatin Jihar, Minna, a ranar Litinin 01 ga Satumba, 2025.
Gwamna Bago ya yaba da gudummawar da mambobin majalisar suka bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a ayyukan da za su gudanar a nan gaba.
