Featured
Ban Gaji Wata Dukiya Daga Wajen Mahaifina Ba – Dangote
Shahararren attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa bai taɓa dogara da gadon dukiya daga mahaifinsa ba wajen gina kasuwancinsa. Ya ce duk abin da yake da shi a yau ya samo shi ne daga ƙoƙarinsa da jajircewa, ba wai daga gadon gidansu ba. Dangote ya bayyana haka ne a wata hira da aka ɗauka tun ranar 8 ga Janairu, 2020, wacce tashar Bloomberg ta wallafa, kuma ta sake bayyana a yanar gizo kwanan nan.
Dangote ya ce kakansa na uwa, Alhassan Dantata, ya kasance mafi arziki a Afirka ta Yamma a shekarun 1940, haka nan kuma kakansa daga ɓangaren uba yana cikin attajiran Najeriya a wancan lokaci. Duk da cewa mahaifinsa ya kasance mai hali daga harkokin kasuwanci da siyasa, Dangote ya ce ya ƙi karɓar dukiyar gadon da aka bari masa. A cewarsa, “Na gaji wasu kadarori daga wurin mahaifina amma tun daga wancan lokaci na bayar da su fisabilillah.”
Ya kuma tuna yadda ya fara tafiyar kasuwancinsa ta hanyar aiki da ɗan uwansa na kusa, kafin daga bisani ya koma Legas, inda ya shiga harkar saye da sayar da siminti. Dangote ya ce ya ga gibin da ake da shi a fannin gine-gine da muhallin zama, inda Najeriya kaɗai ke da buƙatar gidaje sama da 17,000. Wannan ne ya sa ya ga dacewa wajen saka hannun jari a masana’antar siminti wacce a wancan lokaci aka fi dogaro da shigo da ita daga ƙasashen waje.
A yau, Dangote ya kafa kamfaninsa mai suna Dangote Group, wanda ya ƙunshi rassa fiye da 15 a ƙasashe sama da 10 a nahiyar Afirka. Kamfanonin da suka shiga kasuwar hannayen jari sun haɗa da Dangote Cement Plc, Dangote Sugar Refinery Plc da NASCON Allied Industries Plc. Baya ga haka, ya shiga manyan fannonin masana’antu irin su mai da iskar gas, taki, sinadarai, ƙarafa, sufuri, da harkokin gine-gine – abin da ya tabbatar da shi a matsayin ginshiƙi wajen ci gaban tattalin arzikin Afirka.
