Connect with us

Featured

Mamakon Ruwan Sama Da Za’a Yi Zai Iya Haifar Da Ambaliya A Jihohi 15 A Najeriya

Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta fitar da gargaɗi ga jihohi 15 cewa daga 4 zuwa 8 ga Satumba, 2025, wurare 43 a fadin ƙasar na iya fuskantar ruwan sama mai ƙarfi wanda zai iya jawo ambaliya. Wannan sanarwar ta fito ne daga Sashen Kula da girgizar kasa da Ambaliya na ma’aikatar, tare da bayyana cewa matsalar ambaliya na ci gaba da zama babban ƙalubale a Najeriya saboda ta na jawo asarar gonaki, gidaje da kuma haifar da cututtukan.

Jihohin da aka fi hasashen matsalar sun haɗa da Ebonyi (Afikpo), Cross River (Edor, Ikom, Itigidi, Akpap), Kano (Gwarzo, Karaye), Zamfara (Anka, Gummi, Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi, Bukkuyum), Taraba (Dampar, Gassol, Gembu, Mutum Biyu da sauransu), Abia (Eziama, Umuahia), Yobe (Geidam, Kanama, Potiskum), Plateau (Langtang, Shendam, Wase), da wasu sassa na Borno, Imo, Niger, Sokoto, Kaduna da Akwa Ibom.

A halin yanzu, gwamnatin tarayya ta samu tallafin dala miliyan ɗaya daga gwamnatin kasar Sin domin taimakawa mutanen da ambaliya ta shafa a arewacin Najeriya. Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tallafin tare da Jakadan Sin a Najeriya, Yu Dunhai. Bagudu ya ce tallafin zai taimaka wajen isar da kayan agaji da farfado da rayuwar al’ummomi, tare da tabbatar da gaskiya da ingantaccen tsarin kulawa.

Jakadan kasar Sin ya nuna goyon bayan ƙasarsu ga Najeriya, inda ya ce Sin da Najeriya na tare a lokacin wahala da sauƙi. A gefe guda kuma, Hukumar Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta ruwaito cewa za a samu ruwan sama da hadari a jihohi da dama, musamman a arewacin Najeriya, inda ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliyar gaggawa a Bauchi, Jigawa, Katsina, Kaduna da Kano.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet