Featured
Daliban Najeriya Sun Rungumi Amfani da Fasahar AI Domin Karatu — Google
Daliban Najeriya suna ƙara amfani da fasahar wucin gadi (AI) wajen tallafa musu a karatu, in ji sabbin bayanan binciken Google da aka fitar a ranar Talata yayin da makarantu suka koma aiki a fadin ƙasar. Kamfanin ya ce bincike da ya haɗa “AI + studying” ya tashi da fiye da kashi 200 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2024, alamar cewa ɗalibai ba wai kawai suna son sani game da AI ba ne, har ma suna amfani da shi a matsayin abokin karatu.
Google ta bayyana cewa akwai ƙaruwa a binciken “AI + chemistry” da kashi 50 cikin 100, yayin da “AI + mathematics” da “AI + languages” suka tashi da kashi 30 cikin 100 kowannensu. Haka kuma tambayoyi irin su “menene mafi kyawun AI wajen warware matsalolin lissafi?” sun yi yawan gaske. Daraktan Google West Africa, Olumide Balogun, ya ce hakan ya nuna cewa ɗaliban Najeriya suna amfani da AI ba kawai wajen samun amsa ba, har ma don zurfafa fahimtar ilimin kimiyya da lissafi.
Binciken ya kuma nuna cewa sha’awa ga AI ta zarce fagen makaranta kadai. Tambayoyi irin su “yaya ake amfani da AI” da “cikakken ma’anar AI” sun karu da kashi 80 cikin 100, yayin da “wanene uban AI” ya karu da kashi 70 cikin 100. A gefe guda, binciken “AI detection” ya haura da kashi 290 cikin 100, abin da Google ta ce yana nuna yadda ake tattauna batun amfaninsa cikin gaskiya da kare mutunci a ilimi.
Har ila yau, matasa ‘yan Najeriya suna nuna sha’awa wajen amfani da AI don sana’o’i na gaba. Kalmar “Generative AI” ta zama abin bincike sosai a cikin watanni 12 da suka gabata, galibi tana hade da “professional certification”. Wannan yana nuna cewa matasan ƙasar suna shirye-shiryen tunkarar kasuwar aiki ta gaba. Google ta kammala da cewa bincike kan AI a Najeriya ya kai kololuwa a shekarar 2025, inda ya karu da kashi 60 cikin 100 a shekara guda.
