Connect with us

Featured

NABTEB Ta Saki Sakamakon Jarabawar NBC/NTC Ta 2025

Hukumar (NABTEB) ta fitar da sakamakon jarabawar NBC/NTC na watan Yuni/Yuli na 2025, inda aka samu ci gaba sosai wajen yawan ɗaliban da suka rubuta da kuma nasarorin da suka samu idan aka kwatanta da shekarar 2024. Babban Jami’in Hukumar, Dr. Mohammed Aminu Mohammed, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

A cewar hukumar, dalibai 92,875 ne suka yi rajista a cibiyoyi 1,892 a fadin ƙasar, wanda ya nuna ƙaruwa da kaso 37 cikin ɗari idan aka kwatanta da bara. A cikinsu, 89,621 aka tantance, inda 61,104 (kaso 68.18) suka samu Credits biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi. Haka kuma, sama da kaso 83 cikin ɗari sun samu credits biyar ko fiye da Turanci ko Lissafi ko babu. A wannan shekarar, kashi 93.10% sun ci Turanci, yayin da Lissafi ya samu nasarar kashi 94.60%.

Sai dai hukumar ta lura cewa yawancin ɗalibai sun fi cin nasara a Lissafi fiye da Turanci idan aka kwatanta da bara. A gefe guda kuma, an samu raguwar laifin karya doka a jarabawa, inda aka kama ɗalibai 435 da ke da hannu a aikata laifuka 516, idan aka kwatanta da ɗalibai 349 da laifuka 524 a shekarar 2024.

Hukumar ta kuma sanar da buɗe rajistar jarabawar watan Nuwamba/Disamba 2025 na NBC/NTC da ANBC/ANTC. Dr. Mohammed ya jaddada muhimmancin karatun sana’o’i da fasaha (TVET) a tattalin arzikin zamani, inda ya ce a ƙarni na 21 ilimin sana’a da fasaha na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ci gaba da kirkire-kirkire.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet