Addini
Hajjin 2025 Yana Daga Cikin Hajji Mafi Nasara A Tarihin Najeriya – Shugaban NUJ
Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), Kwamared Alhasan Yahya Abdul, ya bayyana cewa aikin Hajjin 2025 ya kasance ɗaya daga cikin mafi nasara da aka taba gudanarwa a tarihin Najeriya. Ya yi wannan bayani ne a wajen taron bita da karramawa na bayan Hajji, wanda Independent Hajj Reporters suka shirya a zauren Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Abdul ya ce, duk da ƙalubale da matsin lamba na lokaci, an gudanar da aikin Hajji cikin nasara tare da tabbatar da cewa ba wani ɗan Najeriya da ya rasa damar yin ibadar. Ya jaddada cewa tsari da kulawar hukumomi, musamman hukumar NAHCON, sun taimaka wajen ganin komai ya tafi lafiya.
Sai dai shugaban ya yi gargadi ga alhazai da ‘yan siyasa da su guji ɗora tallace-tallace ko yin tarukan siyasa a lokacin aikin Hajji, yana mai tunatar da cewa hukumomin Saudiyya ba sa lamunta irin waɗannan ayyuka.
Ya kuma shawarci ‘yan jarida masu ruwaito aikin Hajji da su kiyaye mutuncin ƙasar su a wajen aikin, tare da bin tsarin da kundin tsarin mulki ya shimfiɗa, wato riƙe shugabanni da lissafi. A cewarsa, aikin Hajjin 2025 an samu nasara sosai, kuma ana fatan na gaba zai fi haka.
