Featured
Sojojin Najeriya Sun Lalata Haramtattun Matatun Mai 9 Tare Da Kama Masu Fasa Bututun Mai 17 a Yankin Neja Delta
Dakarun Rundunar Sojin Najeriya na runduna ta 6, sun kama mutane 17 da ake zargin masu fasa bututun mai ne, tare da lalata haramtattun matatun mai guda tara a sassa daban-daban na yankin Neja Delta. Rundunar ta bayyana cewa dakarunta sun kuma kwato sama da lita 45,000 na man fetur da aka sace a wani samame na kwanaki 12 da ta gudanar.
A jihar Delta, dakarun sun gano wata babbar ma’ajiyar ƙarfe a Ogwu, Warri South LGA, wadda ke ɗauke da lita 20,000 na man dizal (AGO) da kuma motar tanka mai ɗaukar lita 20,000 wadda ke cike da man da aka tace ba bisa ka’ida ba. Sun kuma samu injinan tatsa da na aunawa da sauran kayan aikin fasa bututun mai.
Haka kuma, a Bayelsa dakarun sun lalata haramtattun matatun mai guda biyu a Biseni tare da tono rumbunan kasa uku da ke dauke da lita 7,000 na man da aka sace. Sun kuma kama motar Toyota Camry cike da lita 600 na man AGO a Okordia. A Rivers, sun tare Toyota 4Runner mai dauke da lita 1,600 na man da aka sace, sai dai tuni direban ya tsere.
Bugu da kari, sojojin sun gano buhuna 23 dauke da lita 690 na man dizal a Ogbogolo, sun kuma dakile kwale-kwalen katako dauke da man da aka sato a Degema, tare da gano ɓangaren bututun kamfanin Oando da aka lalata a Ogba/Egbema/Ndoni LGA. Rundunar ta ce a Jihar Akwa Ibom dakarunta sun ci gaba da sintiri don hana ‘yan fasa bututun mai samun damar yin ayyukansu.
