Featured
Tattalin Arziƙi: An sace Ɗanyen Mai Da Darajarsa Ta Kai Dala Biliyan 46 a Najeriya – Bincike
Najeriya ta yi asarar gangar danyen mai kusan miliyan 619.7 wanda darajarsa ta kai dala biliyan 46.16 tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020, a cewar wani sabon rahoto na ƙungiyar Fair Finance Nigeria (FFNG). Rahoton mai taken “Community Voices on Oil, Finance, and the Petroleum Industry Act (PIA)” ya bayyana yadda rashin ingantaccen kulawa, cin hanci da rashawa, da kuma hannun wasu jami’an tsaro da kamfanonin mai suka bai wa masu satar mai damar gudanar da wannan barna a matakin masana’antu. Wannan matsala, in ji rahoton, ta janyo babbar asara ga tattalin arzikin ƙasa tare da ƙara fatara a yankunan da ake hako mai.
Ƙungiyoyin da suka haɗu cikin FFNG sun haɗa da BudgIT, CISLAC, CODE, Oxfam, Policy Alert da STEPS, tare da tallafin hukumar ci gaban ƙasashen Sweden (Sida). Duk da cewa man fetur da iskar gas sun kai kaso 89.23 cikin 100 na fitar da kaya zuwa ƙasashen waje a shekarar 2023, amma ba a samun wata fa’ida ga al’umman da suke makwabtaka da wuraren hakar mai. Rahoton ya kuma nuna cewa duk da samun lamuni sama da dala biliyan 10 daga cikin gida da kasashen waje tsakanin 2020 zuwa 2023, yawancin al’umman Akwa Ibom da Bayelsa na fama da mummunan gurbatar muhalli, talauci, da rashin ci gaban da ya dace.
Rahoton ya ƙara bayyana cewa duk da tanadin dokar PIA na 2021 da ya wajabta kamfanonin mai su rika biyan kudi zuwa asusun ci gaban al’umman masu masaukin mai (HCDTs) da aka kiyasta tsakanin $500m zuwa $800m a shekara, an biya dala miliyan 21.753 kacal tsakanin 2022 da 2023. Wannan gibi ya janyo tsaiko wajen aiwatar da ayyukan ci gaba, lamarin da ya kara tsananta halin rayuwa a yankin Neja-Delta. Darakta Janar na CISLAC, Auwal Rafsanjani, ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa wajen magance satar mai tare da tabbatar da gaskiya da adalci wajen amfani da kudaden da ake samu daga harkar man fetur.
A nashi bangare, Daraktan shirye-shirye na CODE, Agu Kingsley, ya jaddada muhimmancin saka idon cibiyoyin kudi wajen hana “greenwashing” ta hanyar bin ƙa’idojin muhalli da gudanarwa (ESG). Ya bayyana cewa tsakanin 2020 zuwa 2023, NNPCL ta samu dala biliyan 8.6, wanda ya taimaka mata ta samu riba har $1.7bn a 2023, duk da cewa rabin bankunan da ke daukar nauyin harkar mai ba sa bin ƙa’idojin ESG yadda ya kamata. Ya bukaci ƙarfafa dokoki da tsauraran matakai na bincike don tabbatar da daidaito tsakanin ci gaban ayyukan mai, kare muhalli da kuma bukatun al’umman yankunan da ake hakar mai.
