Featured
Yajin Aikin PENGASSAN Ne Ya Haddasa Tsadar Gas Ɗin Girki — NNPC
Babban Jami’in Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), Mista Bayo Ojulari, ya danganta tashin farashin gas ɗin girki da aka gani kwanan nan da ɗan gajeren tsaikon da aka samu a lokacin yajin aikin da Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Harkokin Man Fetur (PENGASSAN) ta gudanar. Ojulari ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai bayan ganawar sa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Lahadi 05 ga Oktoba. Ya ce yajin aikin ya dakatar da ayyukan lodi da rarraba gas na tsawon kwanaki biyu zuwa uku, wanda hakan ya haifar da tashin farashi na wucin gadi.
A cewar Ojulari, yayin da yajin aikin ya tsaya, motsi da lodi sun tsaya cak, lamarin da ya jinkirta isar da kayayyaki zuwa kasuwanni. Ya bayyana cewa wannan tsaiko ne ya janyo karuwar farashi, ba wai karancin gas ne na gaskiya ba. Ya ce da zarar harkokin sufuri da rarrabawa suka koma yadda aka saba, farashin gas zai fara raguwa a hankali har ya dawo yadda yake a da.
Bugu da ƙari, Ojulari ya zargi wasu ‘yan kasuwa da amfani da damar tsaikon don su ƙara farashi ba bisa ƙa’ida ba. “Kamar yadda kuka sani, a Najeriya, wasu mutane suna amfani da irin waɗannan lokuta don su yi cuzgunawa talakawa,” in ji shi. Ya tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa farashin gas zai dawo daidai nan gaba kadan bayan tsarin rarrabawa ya daidaita gaba ɗaya.
Yajin aikin PENGASSAN ya samo asali ne daga korar wasu ma’aikata a Gidajen Man Dangote, inda ƙungiyar ta shiga yajin aiki a matsayin martani. Sai dai an dakatar da yajin aikin a ranar 1 ga Oktoba bayan shiga tsakani daga gwamnatin tarayya. Ojulari ya ce yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Dangote Group da gwamnati ta sa ma’aikatan da aka korar suka koma aiki, lamarin da ke rage cunkoson hanyoyin samar da gas a yanzu.
