Connect with us

Featured

Kungiyoyin Ma’aikatan Jami’a SSANU da NASU Za Su Gudanar da Zanga-zanga a Faɗin Najeriya

Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantu ta Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi Masu Alaƙa da Jami’o’i (NASU) sun bayyana shirinsu na gudanar da zanga-zangar kwana ɗaya a ranar Alhamis 09 ga Oktoba, don nuna rashin jin daɗinsu kan gazawar gwamnatin tarayya wajen cika alƙawuran da aka yi musu.

Kungiyoyin, ƙarƙashin haɗin gwiwar JAC, sun umarci dukkan rassansu su gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba domin tattara mambobi don halartar zanga-zangar. Ayyukan za su haɗa da gangami a cikin jami’o’i, ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, da kuma taron manema labarai.

Matsalolin da suka jawo wannan mataki sun haɗa da rabon kuɗin alawus N50bn cikin rashin adalci, jinkirin sabunta yarjejeniyar 2009, rashin biyan watanni biyu na albashi, bashin karin albashi na kashi 25 da 35 cikin 100, da kuma kin tura kuɗaɗen ɓangare na uku na Mayu da Yuni 2022. Kungiyoyin sun ce duk da ƙarin wa’adin da suka bai wa gwamnati, babu wani ci gaba mai ma’ana da aka samu.

Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, ya zargi gwamnati da rashin gaskiya, yana mai gargadi cewa za su iya tsunduma cikin yajin aiki na sai baba ta gani idan bukatunsu ba su samu amsa ba. Ya ce ma’aikatan da ba na koyarwa ba su fi kowa fama da matsin tattalin arziki da rashin kulawa a jami’o’in ƙasar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantsekabetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibommatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet