Connect with us

Addini

Saudiyya Ta Ragewa Najeriya Kujerun Hajjin 2026

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana cewa hukumomin Saudiyya sun rage yawan kujerun da aka ware wa Najeriya daga 95,000 zuwa kusan 67,000 a aikin Hajjin shekarar 2026. Wannan mataki, kamar yadda hukumar ta bayyana, ya samo asali ne bayan da Najeriya ta gaza cike adadin kujerun da aka bata a yayin aikin hajjin 2025, inda aka bar kujeru 35,872 ba a yi amfani da su ba.

NAHCON ta bayyana cewa daga cikin kujerun da aka amince da su a sabon rabon, 51,513 za su tafi ne ta hannun jihohi da hukumomi, yayin da 15,397 za su tafi ne ta kamfanonin yawon bude ido. Hukumar ta kuma sanar da cewa rabon kujerun jihohi zai dogara da yadda kowace jiha ta cika nata a bara, inda jihohin da suka kasa cikawa za su fi fuskantar ragi.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya bukaci haɗin kai tsakanin hukumomi da jihohi domin guje wa matsaloli a shirye-shiryen Hajjin 2026. Ya kuma bayyana cewa ana kokarin rage wasu kudade don saukaka wa mahajjata, yayin da Babban Bankin Najeriya ke nazarin rage kashi 2% da ake cirewa daga kudin su.

Hukumar ta tunatar da jihohi ranar 21 ga Disamba, 2025 a matsayin ranar ƙarshe wajen tura kudaden mahajjata don amfana da kyakkyawan farashin canji. Ta kuma tabbatar da amfani da ƙa’idar kasa da kasa ta jakunkuna da tsauraran dokokin lafiya, inda masu fama da cututtuka masu tsanani ko mata masu juna biyu ba za su samu damar shiga Saudiyya ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet