Connect with us

Featured

Jami’ar Aliko Dangote Ta Kori Dalibai 34

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Jihar Kano, ta kori dalibai 34 bayan tabbatar da laifin yin maguɗin jarrabawa a bangarori daban-daban. Haka kuma jami’ar ta dakatar da wasu dalibai 13 na tsawon zangon karatu guda, yayin da wasu da dama suka samu takardun gargadi saboda irin wannan laifi. Wannan na cikin sanarwar da shugaban sashen bayanai da hulɗa da jama’a na jami’ar, Abdullahi Datti, ya fitar a ranar Juma’a 17 ga Oktoba.

Sanarwar ta ce hukuncin ya biyo bayan amincewar majalisar jami’ar da rahoton kwamitin kula da ka’idojin jarrabawa da rashin daidaito a zaman ta na 123 da aka gudanar ranar 9 ga Oktoba, 2025. Rahoton ya kunshi shawarwari kan matakai daban-daban na ladabtar da daliban da aka tabbatar da laifi, don tabbatar da bin ƙa’ida da kare martabar jarrabawa.

Bugu da ƙari, jami’ar ta kafa Cibiyar Kula da Kayan Aiki domin inganta gyara da kiyayewa na kayan karatu da bincike a dukkan sassa da kwalejoji. Cibiyar za ta dinga aiwatar da tsarin gyara kafin lalacewa, samar da ayyukan gyara ga kayan da suka lalace, tare da shirya horo na yau da kullum ga ma’aikata da dalibai kan yadda ake amfani da kayan aiki yadda ya kamata.

Shugaban jami’ar, Farfesa Musa Yakasai, ya amince da naɗin Dakta Murtala Dambatta daga Sashen Injiniyan Inji a matsayin darakta na farko na cibiyar. Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin jami’ar wajen tabbatar da ingantaccen tsarin karatu da bincike, tare da tsaurara matakai kan duk wani laifi na maguɗin jarrabawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet