Featured
Ƴansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zangar Sakin Nnamdi Kanu
Yan sanda a Abuja sun tarwatsa masu zanga-zangar sakin Nnamdi Kanu a ranar Litinin ta hanyar amfani da hayaƙi mai sa hawaye lamarin da ya sa masu zanga-zangar suka gudu.
An dai girke jami’an tsaro a wasu manyan hanyoyi da muhimman wurare a Abuja, babban birnin Najeriya saboda zanga-zangar.
Masu zanga-zangar dai sun ce niyyarsu ita ce su yi tattaki zuwa fadar Shugaba Tinubu da sauran muhimman cibiyoyin mulki.
Jami’an tsaro ciki har da ‘yan sanda da sojoji da sauransu suka kafa shingayen bincike a kan tituna musamman wadanda suka nufi fadar Aso Rock.
