Featured
Kotu Ta Sanya Ranar Da Za Ta Yankewa Nnamdi Kanu Hukunci
Kotun Tarayya a Abuja ta ayyana 20 ga Nuwamba 2025 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a shari’ar ta’addanci da Gwamnati ke yi wa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Mai shari’a James Omotosho ne ya bayyana hakan bayan karewar kwanaki shida da kotu ta bawa Kanu don ya gabatar da kansa da kariyarsa, amma bai yi amfani da damar ba.
Alkalin ya ce tun da wanda ake tuhumar bai yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya bashi na kare kansa ba, ba zai iya cewa an tauye masa ‘yancin shari’a ba. Wannan ya sa kotun ta kammala sauraron shari’ar tare da jiran hukunci a ranar da ta tsara.
Sai dai a zaman na jiya, Nnamdi Kanu ya shigar da sabon ƙara yana kalubalantar shari’ar gaba ɗaya. Ya ce dokar da aka gina tuhume-tuhumen ta’addanci a kanta an riga an soke ta, don haka babu wani ingantaccen tuhuma da gwamnati za ta dogara da shi a kansa.
Ya nemi kotu ta kori shari’ar tare da bada umarni a sake shi ya koma gidansa, yana mai jaddada cewa babu shaidar da ke tabbatar masa da laifi. Kotu ta ce za a bayyana hukunci a ranar 20 ga watan Nuwamba.
