Featured
Rashin Shugabanci Nagari Ne Ya Haifar Da Matsalar Tsaro a Najeriya – Baba-Ahmed
Tsohon kakakin Kungiyar Dattawan Arewa kuma tsohon hadimin shugaban kasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce matsalolin tsaro da suka yi kamari a Najeriya cikin shekaru goma zuwa goma sha biyar da suka gabata, sun samo asali ne daga jagoranci mara tasiri da ya gaza kare jama’a. Da yake magana a Arise TV, ya bayyana cewa tun bayan gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar’Adua, Najeriya ta kasance cikin jagoranci mai rauni wanda ya bar ƙasar ta fada cikin rikice-rikice masu yaduwa.
Ya ce gwamnoni da shugabannin da suka zo a jere, ciki har da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da mai ci yanzu Bola Ahmed Tinubu, sun kasa magance matsalolin tsaro yadda ya dace, lamarin da ya jawo hauhawar hare-hare, sace-sace, da ta’addanci a sassan kasar. Baba-Ahmed ya bayyana cewa Najeriya ta sauya tsari sosai tun daga farkon bullar Boko Haram a 2009 zuwa yanzu, inda rikice-rikicen suka kara rikitarwa da karuwar sababbin barazana.
Dangane da maganganun shugaban Amurka Donald Trump da ikirarin cewa ‘yan Kirista na fuskantar barazana a Najeriya, Baba-Ahmed ya gargadi cewa shiga tsoma bakin kasashen waje zai iya kara raunana Najeriya. Ya ce Najeriya tana da matsayi na musamman a nahiyar Afrika, saboda haka bai dace a bar wata kasa ta zo ta dora mata hukunci ko ta shigo da karfi.
Gwamnatin Tarayya ta maida martani ga ikirarin Trump, inda ta ce maganar cewa ana kashe dubban Kiristoci karya ce mara tushe. Gwamnatin ta jaddada cewa tana ci gaba da kokarin magance matsalolin tsaro da karfafa zaman tare da sasanci a yankunan da ake fama da tashin hankali.
