Connect with us

Featured

Gwamnatin Legas Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 1 Wajen Biyan Ƴan Fansho

Gwamnatin Jihar Legas ta raba sama da naira biliyan ɗaya ga tsofaffin ma’aikatan jihar 463 da suka yi ritaya daga sassa daban-daban na gwamnatin jiha. Adadin kuɗin da ya kai N1,006,057,173.45 an shigar da shi kai tsaye cikin asusun ajiyar ritaya na ma’aikatan da suka fito daga ma’aikatun gwamnati, ƙananan hukumomi, SUBEB, hukumar koyarwa (TESCOM), da sauran hukumomin jiha.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jiha, Mista Bode Agoro, ya bayyana hakan ne a wajen bikin bayar da takardun shaidar fansho karo na 111 da aka gudanar a NECA Auditorium, Alausa, Ikeja. Ya ce wannan mataki na nuna yadda gwamnatin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ke da jajircewa wajen kula da jin daɗin ma’aikata, masu aiki da wadanda suka yi ritaya.

A jawabin sa, Daraktan Hukumar Fensho ta Jihar Legas (LASPEC), Babalola Obilana, ya ce jajircewar Gwamna Sanwo-Olu wajen biyan fansho akai-akai ta sa Legas ta zama abin koyi ga sauran jihohi a fannin gudanar da fansho. Ya ce duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a duniya, Legas na ci gaba da bin dukkan wajibai ga masu ritaya ta hanyar tsare-tsaren kudi masu inganci da daidaitattun manufofi.

Obilana ya ƙara da cewa LASPEC ta koma amfani da tsarin kwamfuta don tabbatar da gaskiya da saurin aiki a cikin harkokin fansho. A watan Satumba, hukumar ta biya kusan naira biliyan 1.52 ga masu ritaya 798, kuma ta tabbatar da cewa duk wanda ya kammala takardunsa za a biya shi cikin lokaci ba tare da jinkiri ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet