Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Guraben Karatu 50 Ga Ɗaliban Guinea Bissau

Gwamnatin Jihar Kano ta cimma yarjejeniya da gwamnatin Jamhuriyar Guinea Bissau domin ƙarfafa dangantakar aiki a fannoni da suka haɗa da noma, ilimi, al’adu, yawon buɗe ido da kuma bunƙasa ɗan Adam. Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa ta musamman da aka gudanar a birnin Bissau, inda tawagar Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dr. Ajuji Ahmed, ta kai ziyara ga Shugaban ƙasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló, a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

A yayin ganawar, ɓangarorin biyu sun jaddada aniyar su ta haɗin gwiwa wajen samar da ayyukan yi, ƙarfafa matasa da kuma horar da su a sana’o’in zamani. Yarjejeniyar ta haɗa da shirye-shirye a fannin gyaran wayoyin GSM, kiwon kifi, da kuma sarrafa kaju da mangwaro — domin ƙara samar da dama da bunƙasa tattalin arziki.

Haka kuma, gwamnatin Kano ta sanar da bayar da guraben karatu hamsin (50) ga ɗaliban Guinea Bissau domin koyon harshen Turanci da Hausa a jami’o’in jihar, matakin da zai taimaka wajen musayar al’adu da ƙarfafa zumunta tsakanin ƙasashen Yammacin Afirka. Shugaban ƙasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló, ya yaba da hangen nesan Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da bayyana shirinsa na ziyarar amsa gayyata zuwa Kano.

Tawagar Kano ta haɗa da kwamishina Hajiya Amina Abdullahi, mai ba da shawara ta musamman Hajiya Sadiya Abdu Bichi, tsohon shugaban hukumar gyaran birane Arc. Danjuma Zarewa, da Hon. Muhammad Sani Gumel. A cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin Kano za ta ci gaba da neman haɗin gwiwar ƙasashen waje domin samar da dama ga al’ummar jihar, musamman a bangaren ilimi, kasuwanci da al’adu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet